Imam Goni Aisami Yayi Kira Ga Al’ummar Musulmai Da Su Inganta Hadin Kai Da Kuma Ibada Ga Allah Mahalicci.

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani malamin addinin musulunci mai suna Sheikh Ahmad Gumi yayi zargin cewa jami’an sojoji basa son ta’addanci ya kare a kasa saboda wani manufa tasu.

Yayin da yake magana cikin wani hira da akayi dashi a gidan talabijan na Arise,Sheikh Gumi yace wasu manyan jami’an sojojin suna son a cigaba da samun matsalar rashin tsaro sakamakon kudaden da suek samu na kokarin kawo karshen matsalar.

Ya kara dacewa yan fashi da makami a shirye suke da su ajiye makaman su idan har gwamnatin tarayya ta biya musu bukatun su da suka hada da gina makarantu, asibitoci da kuma ingantaccen ruwa.

Yace yan fashi da makami sunyi korafin cewa jami’an soji na kashe jama’an da basu jiba basu gani ba kuma akwai zargin cewa jami’an soji basa son rikicin yakare saboda abin da wasun su suke samu da sunan yaki da ta’addanci.

Daga karshe kuma ya yabawa jami’an yan sanda da sufeta janar na yan sanda bisa kokari da sukayi yayin ziyarar sa zuwa wajen yan fashi da makami.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply