Idriss Deby Jarimin Shugaba Ne Acewar Shugaba Buhari

By:Rakiya Garba Karaye, Maiduguri
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa kan “mutuwar kwatsam da Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya yi a fagen daga, yayin fada da sojojin ‘yan tawaye.

Da yake mai da martani kan lamarin a ranar Talata, Shugaba Buhari ya ce: “Na yi matukar kaduwa da takaici game da mutuwar kwatsam ta Idriss Deby a fagen daga don kare ‘yancin kasarsa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai ya fitar.

A cewar Shugaban, “Marigayi Deby ya taka rawar gani a hadin gwiwar hadin gwiwar yankin da muke da shi a yakin da sojoji ke yi da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Shugaba Buhari ya bayyana marigayi shugaban na Chadi “a matsayin abokin Najeriya wanda ya taimaka kwarai a kokarin fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram da ke haifar da manyan matsalolin tsaro ba ma ga Najeriya ba kawai, har ma da makwabtanmu kasashen Afirka, musamman Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Nijar.

Ya kara da cewa “mutuwar Deby tabbas za ta haifar da babban gurbi a kokarin da ake yi na tunkarar ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma Daular Musulunci ta Afirka ta Yamma.

Yayin da yake jajantawa mutanen Chadi da sabon shugabansu, Shugaba Buhari ya yi kira da a kara yin hadin gwiwa domin fatattakar ‘yan ta’addan.