
Hukumomin kasar Amurka sun amince da amfani da maganin Ebola mai suna remdesivir wajen bawa masu fama da cutar Corona mai tsanani.
An nuna Maganin cewa zai taimaka wajen farfadowar mutane cikin sauki musamman wadanda aka kwantar. Masana kiwon lafiya sunyi kira da a kiyayi amfani da maganin Ebola wanda kamfanin Gilead pharmaceutical company ya sarrafa kuma a dena ganinshi kamar abinda zai yi gaggawar warkar da cutar COVID-19.
shugaban kamfanin Gilead Daniel O’Day ya bayyana yayin day a gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump cewa zasu bada taimakon maganin guda 1.5 don ya taimaka wajen yaki da cutar.

A ranar Asabar da safe kimani mutane 65,603 suka rasu daga cutar coronavirus a Amurka.
