Hukumar Zaben Najeriya Ta Bayyana Cewa Sama Da Jam’iyun Siyasa Guda 100 Ne Suka Shiga Zaben Shekarar 2019

inec2 large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria wato INEC ta bayyana cewa sama da jam’iyun siyasa guda 100 ne suka shiga zaben da za’ayi a shekarar 2019 a cikin kasar.

Wannan bayanin ya fito ne a bakin shugaban hukumar zaben mai zaman kansa farfessa Mahmood yakubu a wajen wani taron karawa junawa sani da wasu kungiyoyi suka shirya a cikin kasar.

Ya kuma kara da cewa ma’aikatan tantance masu shige da fice na kasar sun taimaka wajen gano yan kasashen waje sama 300 wadan da sukayi yunkurin yin register a kasar.

Yakubu ya kuma kara da cewa, addadin wadan da sukayi ragistan a halin yanzu sunkai a kalla mutum miliyan 80 a cikin kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply