Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kwace Magunguna Marasa Inganci Na Kimanin Naira miliyan 80

shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi mairitaya Brig. Gen. Buba Marwa, ya karbi bakuncin shugaban yansanda na kasa ziyara a ofishinsa dake hedikwatar rundunar a Abuja.

hukumar ta kama da kwace kilogram 200 na magungunan da kudinsu yakai naira biliyan 80 inji Marwa.

Marwa ya bayyana hakan yayin da shugaban yansandan yakai masa ziyara a ofishinsa ranar laraba a Abuja, inda yace fiye da yan ta;adda 2,100 ne aka kama da laifukan.

yace suna aikin da damar da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na yaki da miyagun kwayoyi wanda shine sanadiyyar ayyukan ta’addanci.

ya kuma ce hakan ne zai dakile ayyukan ta’addanci a kasar.

a nashi bangaren shugaban yansandan Usman Baba ya yabawa hukumar da yadda take kama abubuwan.

Haka nan yace hadin gwiwa tsakanin hukumonin 2 zai sa a samu nasara a ayyukan kamar yadda aka samu yayinda shugaban yayi kwanaki 100 da kama aiki.