Hukumar Yaki Da Cuttuka Masu Bazuwa Ta ce Ana Samun Karancin Gwaji A Wasu Jihohi.

NCDC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar yaki da cuttuka masu bazuwa sun bayyana cewa ba’a yin gwaji na cutar covid 19 a wasu jihohi kuma hakkan zai sa baza agane barnar da cutar takeyi ba bare a dauki mataki.

Shugaban hukumar Dr Chikwe Ihekweazu shine ya bayyana hakkan a wajen taro a birnin tarraya Abuja.

Ihekweazu ya bayyana jihohi da ake samun karancin gwaji sun hada da jihohin, Jigawa, Kogi, Osun, Ebonyi Adamawa da kuma Zamfara.

Ya kuma kara da cewa gwajin nada mutukar Amfani domin a san yadda za’a shawo kan cutar da kuma taimakawa shirin samanr da rigakafi.

Shugaban ya bayyana cewa jihohin lagas, kaduna da kuma birnin tarraya suke dauke da mafi yawan masu cutan.

Ihekweazu yayi gargadi ga jama’a da su kiyaye dokokin kare kai a yayin da bikukunan karshen shekaran suke karasowa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply