Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Hukunta Mutane 865 Cikin 1,305

efcc-e1466942426836
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da rashawa EFCC, Mohammed Umar Abba ya ce Hukumar ta samu hukunta mutane 865 cikin 1,305 da ta shigar a kotu a shekarar 2020.

Ya ce ana cigaba da bincike a kan kararraki 7,340 a cikin kararraki 10, 152 da Hukumar ta samu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban yada labarai na hukumar Wilson Uwujaren ya sanyawa hannu.

Mukaddashin Shugaban Hukumar ta EFCC ya kara da cewa, Hukumar ta kuma gano kudaden da aka kwato tare da kwace dimbin kadarori daga hannun mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Abba, wanda ya bayyana hakan a sakonsa na karshen shekara, ya kuma godewa ma’aikatan hukumar kan kwazo kan aiki da sadaukarwa da suke yi wajen gudanar da ayyukansu.

Abba ya kuma bayyana hanyoyin da hukumar zata fadada ayyukanta, tare da hadin gwiwar da sauran hukumomin tsaro domin karfafa aiyukansu.

sannna ya kuma umarci ma’aikatan da su jajirce wajen yaki da rashawa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply