Hukumar Wayar Da Kan Jama’a Na Kasa Ta Bukaci Shuwagabannin Addinai Dasu Kaunaci Juna.

noa
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar wayar da kan jama’a na kasa NOA ta bukaci shuwagabannin addinai dasu kaunaci juna, su kuma yi hakuri da juna domin tabbatar da tzaman lafiya tsakanin addinai a kasa.

Darakta janar na hukumar Dr Garba Abari ne ya bayyana hakan yayin taron wayar da kai da hukumar hade da cibiyar labaru da bayanai ta shiryawa shuwagabannin addinan.

Mrs Mette Edokobi, darakatar ayyuka n musamman ne ta wakilce sa inda ta kara da cewa an shirya taron ne domin farkar da shuwagabannin addinai game da nauyi na musamman da suke dashi a cikin al’umma na gina zaman lafiya tare da kwatanta su da cewa a nahiyar afirka da duniya gabadaya suna da matsayi na musamman.

Tace suna da iko da zasu kawar da rashin da’a, kalaman batanci, laifuka, labaran karya da sauran su tare da shawartar cewa suyi amfani da majalisar su wajen ilmantar da jama’a.

Shi kuwa Mr Chido Onumah, shugaban cibiyar na AFRICMIL, yace manufar su shine cimma zaman lafiyar addini tsakanin yan Najeriya da kuma yadda shuwagabanin addinai dana gargajiya zasuyi amfani da bayanai da labaru wajen isar da sakonnin su ga jama’a
Shugabar Jamatul Nasiru Islam bangaren mata na reshen jihar Benue, Hajia Hauwa Isah, tace ya kamata shuwagabanin addinai su zama masu furta alheri yayin isar da sako ga jama’a.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply