Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Bukaci Yan Najeriya Dasu Dinga Bada Rahotannin Tsaro.

civil-defence-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar tsaron farin kaya ta bayyana cewa gwamnati da jamian tsaro kadai baza su iya kawo karshen matsalar tsaro ba har sai yan kasar baki daya sun taimaka musamman wajen bada bayanan sirri.

Darakta Janaral na hukumar ta DSS Yusuf Bichi ne ya bayyana hakan inda ya bukaci yan Najeriya dasu daina ganin laifin jamian tsaro kadai ya kamata su basu taimako don dakile dukkanin muggan laifuka a kasar.

Peter Afunanya mai Magana da yawun hukumar ne ya wakilci Darakta janaral din yayin taron da aka gudanar a hutun mako kan shaanin tsaro da bada ayyukan gaggawa wanda aka gudanar a dakin taro na Nicon Luxury hotel dake Abuja.

Haka nan yace shaanin tsaro ban a gwamnati da jamian tsaro kadai bane ya kamata akwai hadin gwiwa.

San nan ya bukaci yan Najeriya dake gida dama wadanda ke kasashen waje dasu dinga bawa gwamnati hadin kai don a samu a shawo kan shaanin tsaro wanda shine mafarkin Najeriya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply