Hukumar Rayawa Da Bunkasa Cigaban Arewa Maso Gabas Ta Rabawa Manoma Irin Shinkafa, Taki Da Sauran Abubuwa Noma

farmer small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar mai kula da cigaban arewa maso gabas, ta tallafawa manoma da irin shinkafa, taki da magungunan kula da kayan gona da sauran su a jihar bauchi.

Yayin da babban darakatan na hukumar muhammed alkali ke magana, yace an gabatar da shirin domin magance matsalar da ta shafi bangaren noma. Yace, kayyakin sun hada da buhun irin shinkafa 1,500, buhun taki 4,500 dakuma kwalaban magungunnan 1,965.

Hukumar ta kara da sake rabawa makarantu, mutane da sauran cibiyoyi takunkumin hanci guda 24,000 a matsayin hanya ta karewar kai da kamuwa da cutar covid-19.

Sauran kayyayakin sun hada da man wanke hannu da na’urar wanke hannu na zamani zuwa makarantu, kungiyar masu sufiri da dakarun sojoji.

Daraktan yace hanyoyin dasuka dauka yana dai-dai da muradun ma’aikatan wanda yazo dai-dai dana gwamnati wurin hana yaduwar cutar covid-19.

Yayi kira da cibiyar da ta taimakawa gwamnatin jihar wurin daukan kwararun malaman gona domin wayewa manoma kai sabida inganta tsarin noma.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply