Hukumar lafiya Ta Duniya Tace Zata Canza Tsare Tsaren Anfani Da Rigakafin Cutar Shawara.

wHO-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar lafiya ta duniya tace zata canza tsare tsaren na anfani da rigakafin cutar shawara yayin aikin gaggawa sakamakon sabon bayanai.

Sakamakon bayanan kwanan nan wanda kungiyar Medecins Sans Frontiers ta fitar da aka bayyana a cibiyar bincike ya nuna cewa rigakafin da ake yiwa mutane na cutar yana anfani yayin aikin gaggawa.

Wannan ya fito ne cikin wata sanarwa da jami’in sadarwa Abdulkareem Yakubu ya fitar.

Gwaje gwaje ya nuna cewa bada rigakafin yafi kuma zai kawo sauki ga gwamnati da kungiyoyin kasa da kasa domin kare mutane daga ciwon yayin bullar sa wajen karancin maganin rigakafi.

Kodinetan kungiyar Medecins Sans Frontieres ta kasa da kasa Myriam Henkens tace rigakafi shine hanya mafi dacewa wajen kariya daga cututtuka da kuma kiyaye yaduwar sa idan ya bullo.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply