Hukumar Kula Da Yan Gudun Hijira Zata Gina Gidaje 600 A Kauyen Amarwa Dake Karamar Hukumar Konduga A Jihar Borno

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar al’amuran yan gudun hijira, zata gina gidaje dari 6 a kauyen Amarwa dake karamar hukumar Konduga na jihar Borno domin bada mafaka ga yan gudun hijira dubu 45 da suka koma mahaifar su.

Sanata Basheer Mohammed kwamishinan na hukumar yayin sanar da da komawar yan gudun hijirar zuwa mahaifar nasu yace gidaje shine babban matsalan day an gudun hijrar ke fuskan ta wanda yace miliyoyin yan gudun hijira ne suke mafaka a sansaononin yan gudun hijira cikin jihar Borno da kuma na kananan hukumomin Monguno, Dikwa, Gwoza, Bama, Banki da Pulka.

Yayin kaddamar da shimfidar ginin, gwamnan Zulum yace gine-gine da akeyi a hanyar Maiduguri zuwa bama akalla zai dauki yan gudun hijira miliyan 2 wanda da zaran an gama ginin zai taimaka wajen rage matsalolin matsuguni day an hijira ke fuskanta a manyan bianai.

Gwamna Zulum ya kuma yin alkawarin hada da hukumar don kamala gine-gine akan lokaci inda yace rahoton da bankin duniya da kuma gwamnain tarayya dana jihaa suka fitar ya nuna gidaje sama da dubu dari 4 ne yan ta’adda suka lalata kuma ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya bias kokarin ta a bangaren mayar day an gudun hijirar mahaifar su.

Haka zalika sanata yaayi rabiyar kayan abinci gay an gudun hijirar da suka koma a Kawuri, yace anyi makamancin hakan a jihar Kawuri Katsina sanna n ana kokarin yi a jihohin Edo da Zamfara.

Haka zalika ya mika godiyar sa ga shugaban kasa da gwamnan jihar Borno bisa kokarin su kuma myace suna sa ran ayyuka zai kare a karshen sheakarar nan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply