
Hukumar kula da katin dan kasa ranar alhamis ta bayyana hanyoyin rage taron yawan mutane wajen yin rejista a kasar.
Wannan yana cikin hanyoyin da hukumar ta dauka wajen hana yaduwar cutar ta corana virus wanda ministan sadawar Isa Pantami ya bayyana.
Hanyoyin sun hada zuwa ofisoshin dake kusa da mutane a lokacin awannin aikin.
Gwamnatin tarrayya ta hanyar hukumar sadawar ta bada sati biyu domin kowa yayi rejista layyukan waya domin kada a yanke shi.
Hukumar tace akwai hanyoyi da dama don mallakar layin waya wanda tace an shigo da tsarin ne dan magance rashin tsaro da kuma laiffufuka wanda ya hada da yanar gizo. Kuma sun ce Boko Haram tana amfani da layin wayoyi ta hanyar yadda bai dace ba.

