Hukumar kidaya Ta kasa Ta Bukaci Gwamnatoci A Dukkan Matakai Da Su Karfafa Matasa A Bangaren Ilimi

images (45)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar kidaya ta kasa ta bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su karfafa matasa, bangaren ilimi da kuma samar da kayyakin bukata na kiyasce iyali.

Shugaban kwamitin Nasir Kwarra ne ya bayyana hakan yayin mika wani rahoton bincike a Abuja
Binciken wanda hukumar tare da cibiyar ilimi na John’s Hopkins suka gabatar zai bada rahoton yadda za’a inganta yanayin kasar.

Nasir yace rahoton binciken ya nuna kididdigar yan najeriya miliyan 214 ciki kashi 63.5 matasa ne yan kasa da shekaru 25.

Yace sai fa an sauki kwararrun matakai wajen saka matasan a ayyukan koyon sana’o’i, da cigaba, dma bangaren lafiya da sauran su domin kawar da kasar daga fuskanta matsaloli.

Sakataren kasafi, da tsare-tsaren kasa Mrs Olusola Idowu cikin jawabin ta, ta gode musu da binciken kuma tace za’ayi amfani da sakamokon wajen yin tsaren-tsaren tattalin arzikin kasa sannan tayi kira ga saura gwamnatoci dasu kwaikwayi hakan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply