
Hukumar Hisbah na jihar Bauchi ta kama wasu matasa 6 wadanda suka kware wajen shirya taron nuna tsiraici da kuma tada fitina a kauyen Dolam na karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar.
Babban kwamishina da aiwatar da Shari’a na Hisbah Mal. Aminu Idris shi ya bayyana haka yayin hirar sa da kanfanin dillancin labaran Najeriya a Bauchi.
Yace matasan sun kware wajen shirya taro domin rawa wanda ake kira da Gwaidu inda suke sanya kananan y’ammata aikata abubuwan da basu dace ba wani lokacin kuma sukan tursasa su.

Yayin bincike kwamishinan Hisbah na jihar yace sun kira iyayen yaran sun gargade su kuma sun sanya hannu akan sake maimaita wannan laifi da yaran su sukayi.
