Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta bankado gonakin tabar wiwi a kananan hukumomin Gwarzo, Danbatta da kuma Ungoggo na jihar Kano.
Kwamandan hukumar Isa Likita Muhammad shi ya bayyana haka a jihar Kano yayin kaddamar da wani kamfen akan illar shan miyagun kwayoyin da kuma kaddamar da jakadun mata masu yaki da miyagun kwayoyi a jihar.
Yace an samu wannan nasarar ne watannin kadan bayan ya fara aiki a jihar.
Daga karshe ya bukaci jama’ar gari da su goyawa hukumar baya ta wajen bada bayanai da yin yaki da miyagun kwayoyi a jihar.