Hukumar DSS Ta Bayyana Cewa Akwai Wasu Yan Ta’addan Da Suke Shirin Tada Zaune Tsaye A Wannan Biki Na Kirismeti.

DSS thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar tsaron farin kaya ta bayyana cewa akwai wasu yan ta’adda da suke shirin tada fitina a wuraren hada hadar jama’a yayin bikin kirismeti.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta kasa Peter Afunanya ya bayyana a wata sanarwa a Abuja, cewa shrin da akayi na tada fitinar anyi ne ta hanyar tada bama bamai da wasu hanyoyi na anfani da muggana makamai.

Sanarwar ta kara dacewa an shirya hakan ne domin tada hankalin jama’a tare da karya guiwar gwamnati.

Haka kuma sanarwa ta kara dacewa hukumar ba zatayi kasa a guiwa ba wajen fatattakar yan ta’adda ba tare da gurfanar dasu a gaban shari’a.

Daga karshe sanarwar tayi kira ga jama’ar gari das u maida hankali kuma su sanar da duk abin da basu yarda dashi ba ga hukumomin tsaro.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply