Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Kasa Ta Raba Kayaki Ga Yan Gudun Hijira Dubu 30 A Jihar Taraba.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta raba kayaki ga yan gudun hijira dubu 30 a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya.

Darakta janar na hukumar AVM Muhammad Muhammad shi ya bayyana haka yayin kaddamar da kayakin ga mutanen a kananan hukumomi 16 da aka gudanar a Jalingo babban birnin jihar.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar Hafeez Bello ya fitar a ofishin su na Yola.

Darakta janar wanda ya samu wakilcin shugaban ayyuka na hukumar Mr. Maidalla Iliya dake ofishin su na shiyyar Adamawa da Taraba yace kayakin sun hada da abinci dana amfani ya kara dacewa an raba kayaking a magidanta dubu 5.

Ya kara dacewa hakan na da alaka da ma’aikatar bada agaji da walwalar jama’a karkashin minister Haj. Sadiya Farouk domin saukakawa yan gudun hijira a jihar.

Kayakin sun hada da buhun shinkafa mai nauyin kilogram 12 da digo 5 da wake mai nauyin kilogram 25 da man girki, tabarmai, barguna, gidajen sauro da sauran su.

Kuma ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin da kada su dauka gwamnati ta biya su ne, ai dai dan ta saukaka musu radadin da suke ciki.

Tunda farko dai kwamishinan ayyuka na musamman da harkokin agaji na jihar Taraba Mr. Taninga Dinga wanda ya samu wakilcin sakataren ma’aikatar Mr. Samson Tijos ya nuna jin dadin sa bisa ingancin kayakin da hukumar ta samar kuma ya yabawa gwamnatin tarayya bisa taimakon tare da duba bukatar da gwamnan jihar ya mika kan matsalar yan gudun hijira.

A nashi bangaren shugaban karamar hukumar Jalingo Abdulnaseer Bobboji yayi godiya ga gwamna Darius Ishaku kan duba korafin mutanen da rikici ya shafa tare da mikata ga gwamnatin tarayya.