Hukumar Bada Agaji Ta Kasa Ta Shirya Horon Bada Agaji A Jihar Borno

nema 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMAta tabbatar da kokarinta na horar da jami’anta wajen bada agajin gaggawa yain da aka samu iftila’i.

Darakta janaral na hukumar Air Vice Marshal Muhammadu Mohammed mai ritaya ne ya bayyana hakan yayin bikin bude horon na kwana 4 da aka gudanar a da hadin gwiwar Nigerian Red Cross Society reshen jihar Borno.

Daraktan sashin kula da jamaa na hukumar Usman Aji ya wakilci darakta janaral din inda yace horon zai taimaka wajen gina ma’aikatan hukumar.

A nashi jawabin mai kulla da yankin arewa maso gabas a hukumar Ishaya Chinoko yace habbaka rayuwar ma’aikatan abune mai matukar mahimmanci.

Haka nan yace abubuwan dad a zasu koya ya hada da yadda ma’aikatan zasu gane girman abun ko kuma suna cikin hatsari da kuma kula da wadanda suka samu raunuka.

Wakilin hukumar Nigerian Red Cross Society a jihar Borno Babagana Usman yace horon zai karkata kan karfafa ayyukan ma’aikata.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply