Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa Ta Samar Da Sabon Tsari Gudanar Da Aikin Hajji Cikin Sauki.

hajj.jpg 2.jpg 3 x 3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hassan Umar Shallpella
Hukumar aikin hajji ta kasawa ta samar da sabon tsari na masu karamin karfi don samu gudanar da aikin Hajji cikin sauki.

Hajjin dai itace daya daga cikin rukunan Musulinci wanda kuma sabon tsarin na tara kudin aikin Hajjin an samar dashi don saukakawa wajen biyan kudaden a hankali.

Yayin bikin bude sabon tsarin da aka gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa an gudanar dashi ne a cibiyar Nyako dake sakatariyar jihar inda shugabanta na kasa Alhaji Zikirullahi Kunle Hassan wanda Daraktan bada lasisi na hukumar Alhaji Zakariyau Umar ya wakilta yace shirin anyi don samarwa maniyyata sauki.

Shirin nan tara kudin aikin Hajjin wato ‘Hajj Savings Scheme’ anyi hadin gwiwa da bankin Jaiz wanda zai bawa musulmai damar tara kudin a hankali na wani dan lokaci don gudanar da aikin Hajjin.
Yayin da yake jawabi yayin taron shugaban tsare-tsare na hukumar Dr Tanko Aliyu ya bayyana wasu amfanunnuka na tsarin wanda ya hada da tara kudin, samar da ayyuka ga jama’a, rage radadin talauci, da sauransu.

Aliyu ya yabawa gwamnatin jihar Adamawa da hukumar aikin Hajjin ta jihar Adamawan kan taimakon da sukabayar don shirin ya amfani Musulmi a fadin jihar.

A nashi jawabin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar wanda sakataren gwamnatin jihar Mallam Bashir Ahmad ya wakilta yace shirin zai taimakawa masu karamin karfi don gudanar da aikin hajjin nasu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply