Hafsan sojin kasa na Najeriya Attahiru Ibrahim ya sake jaddada irin goyon bayan shuagba Buhari da kuma na rundunar sojan Najeriya wajen kawo karshe ta’addancin BokoHaram a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da yan jaridu bayan ya kammala taro da manya-manyan ma’aikatan rundunar OLD a barikin Maimalari na Maiduguri.
Yace yana yawaita ziyara hedikwatan rundunar old ne domin basu kaimi da kuma nuna irin bada hankalin da hafsan yayi ga rundunar a yakar ta’addanci da sukeyi inda ya kuma albishirin cewa, shugaba Buhari zai bada duk wani abu na bukata a yakar ta’addancin.
A game da hare-haren kwanan nan day an kungiyar Boko Haram suka kai kan wasu runduna a yankin rewa maso gabaas, yace a okuta da dama rundunar tana samun nasara akan ayyukan yan ta’adda kuma yace hakika Najeriya zata shafe yan ta’adda a Najeriya.