Hafsan Sojin Sama Yayi Bikin Kirsimati Tare Da Sojoji.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar ya sake jaddada kudurin sojojinsa na ganin cewa kasar tana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sadique Abubakar na wannan bayanin ne a wajen bude taron kirsimeti da sukayi da sojoji na Operation Lafiya Dole a birnin Maiduguri.

Yace sunyi wannan taron ne domin ragewa sojoji kewa na rashin iyalensu a yayin bikin kirsimati.

Ya kuma kara da cewa bikin zai karfafa zumuci a tsakanin sojojin tare da kuma baiwa sojin dama yabawa junnan su da irin rawar da suke takawa a filin daga. Yakuma yi kira ga sojojin da su kara kaimi.

Shugaban yay aba da goyon baya da suke samu daga shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da kayakin aiki da suka dace.

Gwamna Babagana Umara Zulum wanda mataimakin sa Umar Kadafur, ya wakilta yay aba da rawar da sojin sama suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a cikin jihar dama kasar baki daya.Yace Gwamatin jiha zata mara musu baya akoda yaushe.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply