Hafsan sojin kasa yaba tabbacin inganta walwala, albashi da kuma kayan aiki ga rundunar sojojin Najeriya

Hafsan sojin kasa na Najeriya laptanar janar Ibrahim Attahiru yaba da tabbaci da kuma dukufa kan inganta walwalar su, da ma kayayyakin aiki da albashin ma’aikata da sojojin zasu nema a dukkan fadin Najeriya.

Ya kuma godewa Shugaba Buhari sakamakon kokari daya keyi na kawo karshen ta’addancin Boko Haram dama ayyukan bata gari a Najeriya

Janar Attahiru ya bayyana hakan ne a barikin soji na Maimalari yayin taron salla na musamman da kuma zaga majinyatan rundunar dayayi domin musu gaisuwa inda yace manufar taron shine karfafa kaimin rundunar musamman ma rundunar Hadin Kai.

Komandan rundunar na Operation Hadin Kai, Major Gen. Farouq Yahaya, ya godewa hafsan bisa kaddamar da sabbin gine-ginen rundunar da yayi inda yace hakika sunji dadi karfafa musu dayayi kuma zasu ci gaba da aiki da gaskiya tare da mayar da hankali a yakin nemowa yankin arewa maso gabas zaman lafiya.