Biyo bayan ƙudirin majalisar dokokin hadaddiyar daular larabawa ta UAE mai lamba 83 na 2021, ta zayyana mutane 38 da kamfanoni 15 a matsayin masu tallafawa ta’addanci a cikin ƙasar.
A cewar Al Arabiya News, shawarar wani bangare ne na kokarin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi na dakile hanyoyin sadarwa da ke da alaka da kudaden ta’addanci da hana duk wani shiri da suke da shi.
An umarci hukumomin tabbatar da doka a kasar da su dauki matakan da suka dace kan daidaikun mutane ko hukumomin ko duk wani mai alaka da su.
‘Yan Najeriya shida su ne Abdurrahaman Ado Musa, Salihu Yusuf Adamu, Bashir Ali Yusuf, Muhammed Ibrahim Isa, Ibrahim Ali Alhassan, da Surajo Abubakar Muhammad.
Wasu daga cikin sauran ‘yan ƙasar sune Ahmed Mohammed Abdulla Mohammed Alshaiba Alnuaimi (UAE), Mohamed Saqer Yousif Saqer Al Zaabi (UAE), Hamad Mohammed Rahmah Humaid Alshamsi (UAE), Saeed Naser Saeed Naser Alteneiji (UAE), Hassan Hussain Tabaja (Lebanon) da Adham Hussain Tabaja (Lebanon) da sauransu.
kamfanonin sune Ray Tracing Trading Co LLC, H F Z A Arzoo International FZ E, Hanan Shipping LL.C, Four Corners Trading Est, Sasco Logistic L.L.C, AlJarmouzi General Trading LLC da Al Jarmoozi Cargo ^ ~ aring Clearing (L.L.C).
A shekarar 2020, an daure ‘yan Najeriya shida a gidan yari na shekaru 10 a daular Larabawa saboda bayar da tallafin Boko Haram.
Kotu ta same su da laifin kafa wata kungiyar Boko Haram a Hadaddiyar Daular Larabawa don tara kudade da taimako na kayan agaji ga masu tayar da kayar baya a Najeriya.
Sun daukaka kara kan hukuncin, suna masu jayayya cewa “musu sharri ne”, amma halin yanzu ana nan ana musu hukuncin su.