
Maitamakin gwamnan jihar borno, Usman Kadafur ya kaddamar da rabon injinan nika, keken dinkuna da kudi ga mata 600 a kananan hukumomi guda biyar dake kudancin borno a matsayin hanyar karfafawa kan sana’a , wanda senata Mohammed Ali Ndume ya bayar.
. Taron na karfafawa matan ya gudana a gidan Ambassador Saidu Pindar Biu inda shima ya zama shaida ga kyautar transhoma na wuta da matar senata Mohammed Ali Ndume, Hajiya Maryam Ali Ndume ta bawa mutanan unguwar Galtimari dake Biu tareda kudi naira miliyan uku don taimakon matan yankin wanda matar mataimakin gwamnan Hajiya Maimuna Kadafur.
Mataimakin gwamnan ya roki waddanda suka amfana da wannan taimakon da cewar kada su siyar da kayyayakin, suyi amfani dashi ta hanyar daya dace.

Kananan hukumomin sun hada Biu, Hawul, Kwaya, Bayo da Shani.
