Gwamnonin Arewa Sun Kalubalanci Kansu Da Masu Ruwa Da Tsaki Dasu Dakile Ayyukan Ta’addanci A Yankin

northern-nigeria
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar Gwamnonin Arewa sunyi kira ga sauran gwamnoni da masu ruwa da tsakin yankin don samar da maslaha ga abubuwan da suka addabi yankin na Arewa.

Shugaban kungiyar gwamnonin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Kaduna yayin bude taron.

Yace yankin nasu ne ke dauke da manyan matsalolin da ake fama dasu a kasar ta yanda rayuwa bata da wani mahimmanci a yankin.

Haka nan rahotanni sun nuna yadda aka bar yankin a baya ta fannin ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, samar da abinci, masana’antu da habbaka rayuwar jama’a.

San nan yace duk wadan nan abubuwan sun koma baya sakamakon ayyukan ta’addanci day a adddabi yankin shekau da dama.

Ya kuma ce kungiyar tasu ta rubuta abubuwa 12 da suka addabi yankin don kawo karshensu.

Haka nan Lalong yace duk da wasu abubuwan ba’a saba dasu a yankin na Arewa ba amma yadda zasu dauki hanyoyin magance su a kasar baki daya.

San nan yace hakan ma ya shafi tattalin arzikin kasar da kuma lalata hanyoyin samar da abinci.

Haka nan yayi kira ga wadanda suka halarci taron dasu fadi gaskiya kuma su bayyana duk abubuwan da suka dace a rahotannin da zasu mika.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply