Gwamnonin Arewa Maso Gabashin Najeriya Sunyi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Data Bawa ‘Yansanda Kayan Yaki Da ‘Yan Ta’adda

FB_IMG_1597063088441
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnoni 6 na yankin arewa maso gabas sunyi kira ga gwamnatin tarayya data bawa ‘yansanda dama ta yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas.

Ana fama da ta’addanci yan kungiyar Boko Haram tun shekarar 2009 wanda ya lakume kimanin rayuka fiye da 36,000 da dukiyoyi na fiye da Naira tiriliyan 3 a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Takardar yarjejejniya da shugaban kungiyar gwamnonin na arewa maso gabas gwamna Babagana Zulum na jihar Borno yasa hannu bayan taron da suka gudanar a Maiduguri yace suna rokon gwamnatin ta bawa yansandan damar yadda ta bawa sojoji wajen yakin.

Haka nan sunce idan aka bawa yansandan makaman yakin za’a ga inda ya kamata jami’an sojin su taimaka musu.

Sunce a bawa yansandan kayan aiki kamar barkonon tsohuwa, abunda da zai binciki inda mutum yake, da kuma motocin yaki.

Ranar Asabar ne dai gwamnonin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe suka gana a Maiduguri don duba kalubalen yankin nasu.

Haka nan sunyi kira da a karfafa tsaro a yankunan masu wahalar shiga da gonaki don kar a samu karancin abinci a yankin.

Da suke tattaunawa kan hare-haren yan bindiga a yankin sun bukaci gwamnati data samar da kayan aiki ga sojojin dake yankin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply