Gwamnatin Zata Dinga Duba Yadda Ake Amfani Da Yanar Gizo .

lai-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zata dinga duba yadda ake amfani da kakfen sad zumunta na yanar gizo don samun hadin kai a kasar.

Ministan ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a jihar Legas inda yace gwamnati baza ta nade hannun ta tana gani ana amfani da kafafen sada zumuntar na yanar gizo ba bisa kaida bat a yadda suke tunzura kasar cikin rikici.

Haka nan Mohammed ya tabbatarwa yan Najeriya cewa yayin dakile ayyukan na kafafen sada zumuntar gwamnati bata da niyyar hana amfani da kafar ko hana fadar yancin albarkacin baki kamar yarda wadansu ke fada.

Ministan yace an taba jin tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama yana cewa kafar sadarwar ta zamani tasa an samu babban kalubale a damokaradiyya.

San nan ya bayyana cewa wanda ya samar da shafin Facebook wato Mark Zuckerberg’s yayi kira da a rage amfani da wasu kafafen kamar yadda babban kamfanin kimiyya da fasaha ya amince da bukatar ta Zuckerberg’s.

Haka nan ya bayyana rrashin jin dadinsa na yadda wasu kafafen sadarwa da suka dade cikin aikin jaridar suka dinga bada rahotanni yayin da aka gudanar da zanga-

zangar EndSARS a kasar musamman kan yadda akace jami’an tsaro na kai hari inda yace wan nan abun takaici ne.

Yayin bada rahotanni kan rikicin Ministan yace manema labarai sam basu bada mahimmanci kan yadda bata gari suka kashe jami’an tsaro ta mummunar hanya ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply