Gwamnatin Tarrayya Tace Zata Gyara Matatan Mai Dake Garin Port Harcourt

Gwamnatin tarrayya tace niyyar sake gyaran matatan mai na port harcourt dake jihar rivers ba zai zama babban nauyi ga gwamnatin najeriya ba.

karamin ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva ya bayyana a wani shiri na gidan channels television wanda wakilinmu yake bibiyar shirin
Ministan yace gwamnatin tarayya zata bada dalar amurka miliyan 800 wanda ayanzu an kasa kasha uku.

Gwamanatin ta shirya bada dalar amurka biliyan 1.8 wurin sake farfado da matatar man inda ya kawo cecekuce acikin kasar.

Ministan yace yan kasar kada su rika cecekuce kan irin wadannan ayyukan ba.