Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don tabbatar da gasa a bangarorin da ke samar da kayayyaki, don samar da tattalin arziki mai amfani.
Alh. Abubakar Aliyu, Coordinator, na Nigeria Competitionness Project (NICOP) ne ya bayyana haka ranar Litinin a garin Ibadan a taron sake duba ayyukan na NICOP karkashin shirin Gasar Afirka ta Yamma.
Aliyu, wanda madam Inyang Arit, jami’ar kula da harkokin kudi ta NICOP ta wakilta a taron, inda ta bukaci masu ruwa da tsaki a kan darajar su yi amfani da damar da aikin ya bayar.
A cewarsa, babban burin aikin shi ne karfafa gasa a Najeriya don bunkasa hadewar kasar cikin tsarin kasuwanci na shiyya da na duniya.
Ya ce Shirin Gasar Najeriya (NICOP) na da muhimmanci ta hanyoyi da dama; daya daga cikin mahimmancin shine na saka jari da wadatar rayuwa.Aliyu ya kuma umarci mahalarta taron da su cigaba da karfafa ayyukan nasu kum a su mai da hankali kan kayayyakin za’a dinga gogayya dasu.
Hakazalika, Hajiya Zainab Ahmed, Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, wanda Mista Chamberlain Okoro, Mataimakin Darakta a ma’aikatar ya wakilta ya ce burin shi ne a karfafa gasa a Najeriya.
A nasa jawabin, Dakta Debo Akande, Mai ba Gwamnan Jihar Oyo shawara ta musamman, ya ce Jihar ta shirya tsaf don samar da kayayyakin more rayuwa ga kananan manoma da kuma kananan da matsakaitan masana’antu a harkar noma domin bunkasa abinci.