Gwamnatin Tarayya Ta Rage Farashin Man Fetur.

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur daga naira dari 1 da 68 zuwa dari 1 da 64 da kobo 44 kan lita daya daga ranar 14 ga watan nan.
Ministan ayyuka da walwalar ma’aikata Dr. Chris Ngige shi ya bayyana haka a karshen taro da shuwagabannin kungiyar kwadago.

Farashin man a yanzu da yake dari 1 da 68, ya biyo bayan shawarar da kanfanin masu sayar da man fetur sukayi na kara farashin tsoffin matatan mai daga naira dari 1 da 47 da kobo 57 zuwa naira dari 1 55 da kobo 17 a watan Nuwamba.

Ministan ya kara dacewa rage farashin ba zai shafi farashin danyen man fetur ba sai dai bangaren kanfanin man fetur ta kasa.

Yace an samar da sabon farashin ne da hadin guiwar kwamitin kanfanin man fetur ta kasa da wakilan kungiyar kwadago.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply