Gwamnatin Tarayya Ta Kara Lokacin Yin Rajistar Shedar Zama Dan Kas

images (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya ta kara lokacin yin rajistar shedar zama dan kasa da layukan wayoyi har izuwa ranar 9 ga watan fabrairu na 2020 tsabanin ranar 19 na wannan janairu da ake ciki.

A baya NIMC ta tsayar da ranar 19 ga watan janairun wannan shekara na ryfewa ga wadanda suke da shedar kasa, haka kuma ta tsayar da 9 ga watan fabrairu ga wadanda basu da shedar kasan domin basu daman yi baki daya.

Hukumar ta wallafa hakan ne a a shafin ta na twitter sannan ta bukaci jama’a da su nemi shedar kasa akan lokaci.

Ranar talata, hukumar sadarwar kasa NCC ta fitar da sanarwa wanda darakta ayyuka Dr. Ikechukwu Adinde ya rattaba hannu akai.

Cikin sanarwar Mr Adinde yace sakamakon taro da mambobin kwamitin ayyukan da suka gudanar, sun samu rahoton irin cigaba da aka samu wanda yace an gano jama’a miliyan 47.8 ne sukayi rajistar alakanta layukan wayoyi da shadar kasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply