Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Gina Gidaje 300,000 A Fadin Najeriya

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a shirye take ta gina gidaje 300,000 a fadin Najeriya don taimakawa ma’aikata masu kananan albashi karkashin tsarin National Social Housing Programme.

Gwamnatin ta bayyana hakan a shafinta na twitter inda ta bayyana wa jama’a kudurin na gwamnatin tarayya .

Gwamnatin ta bayyana cewa masu kananan albashin zasu mallaki gidajen cikin sauki a kuma farashi mai rahusa inda zasu amfana da rukunin gidajen 300,000 dama ayyukan yi ga miliyoyin yan Najeriya.

Tsarin samar da gidajen na karkashin tsarin shugaba Muhammadu Buhari na farfafdo da tattalin arziki gay an Najeriya.

Za kuma a gina gidajen 300,000 a dukkanin jihohin kasar ciki harda babban birnin tarayya Abuja inda Najeriya tace tana maraba da wadanda suke da sha’awar hadin gwiwa da gwamnatin wajen gina gidajen.

Dandal Kura Radio ta tuno cewa watanni 3 da suka wuce babban bankin kasar wato CBN ya amince da kudi kimanin naira biliyan 200 do samar da gidajen ga ma’aikata masu karamin karfi karkashin billion Family Homes Fund Limited.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply