Gwamnatin Tarayya Ta Baiyana Ranna Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

images (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Jumaa 25, Litinin 28 ga Disamba 2020 da Jumaa, 1 ga watan Janairu, 2021 a matsayin ranakun hutu domin bikin Kirsimeti, da Sabuwar Shekarar .
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, ya taya Kiristocin da dukkan ‘yan Najeriya dama mazauna ketare murna wannan shekara na Bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.
Aregbesola ya yi kira ga kiristoci dasu dauki akidar yesu Kristi bisa imani, bege da kaunan juna .
Ya kara da cewa zaman lafiya da kaunar juna shine muhimman abubuwan da ake bukata domin baiwa Gwamnati damar cimma burinta na farfado da tattalin arziki, tare da samar da ayyukan yi ga matasa sama da miliyan 100 a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Aregbesola ya shawarci ‘yan Najeriya musamman Kirista, da su bi ka’idoji da hukumomi suka dingaya na kariya daga cutar Covid-19, a wanna lokacin ,karo na biyu na barkewar cutar.

A karshe Ya yiwa daukacin yan Nijeriya da Kirista barka da bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply