
Gwamnatin tarayya tace zata bude makarantu a fadin kasar nan a ranar 18 ga watan nan.
Babban kodinetan kwamitin fadar shugaban kasa kan cutar corona Dr. Sani Aliyu shi ya bayyana haka cikin wani shiri a gidan talabijan.
Ya bayyana abin da ministan ya fada da cewa zasu sake nazari amma ba canza ranar ba kuma zasu sanar da kasar.

