Gwamnatin Kasar Burtaniya Ta Maidowa Najeriya Fam Miliyan 70

Mr Paul Arkwright,
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin kasar Burtaniya ta maidawa tarayyar Najeriya fam miliyan 70 wadanda aka samu wani dan ‘kasar Najeriya da yin sama da fadi da su kamar yadda kotun ‘kasar Italiya ta gano.

A cikin wata sanarwa da babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya Mista Paul Arkwright, ya bayyana cewa tuni gwamnatin kasar burtaniya ta maidawa Najeriya kudin da aka sace.

Jakadan bai bayyana ainihin mai lanfin ba, amma har ila yau yace nan gaba za a sake dawo da ma‘kodan kudaden da aka 6oye a ‘kasar Burtaniya. Ya ‘kara da cewa gwamnatin ‘kasarsa na yin aiki tu’kuru da gwamnatin Najeriya domin ganin an dawo da tarin ‘kudaden da aka sace.

Mista Arkwright, ya kuma bada tabbacin cewa Frai Ministan kasar Burtaniya uwar gida Theresa May, za ta ziyarci ‘kasashen Najeriya, Kenya da kuma Africa ta kudu a wannan makon.

Ziyarar da uwar gida May za ta yi a tarayyar Najeriya wani yunkuri ne na samarwa ‘kasar madogara a sa’ilin da take gab da ficewa daga ‘kungiyar tarayyar Turai.
Tawagar za ta fara ne daga kasar Afrika ta kudu inda za su gana da shugaban kasar Cyril Ramaphosa da kuma sauran shuwagabannin matasa ‘yan kasuwa. A ranar laraba Misis May za ta gana da shugaba Muhammadu Buhari a birnin tarayya Abuja sa’annan ta wuce zuwa jihar Legas.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply