Gwamnatin Jihohin Borno Da Kano Zasu Hada Gaiwa Kan Ilimin ‘Ya Mace.

KANO
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta hada hannu dana jihar Kano wajen daukan nauyin karatun marayu yan mata wanda matsalar ta’addan ya shafa domin ciigaba da karatun su a jihar Kano.

Kwamishiniyar harkokin mata na jihar Borno Haj. Zuwaira Gambo ita ta bayyana haka lokacin da mambobin ‘HeforShe’ Gender Champions suka kawo mata ziyara a Maiduguri, tace shirin shine domin inganta ilimin ‘ya mace da kuma samun karuwar yara mata a makarantar firamare da sakandare da kuma nag aba da sakadare.

Tace akwai yaran mu mata da dama da sanadiyyar ta’addanci suka bar makaranta, kasancewar su marayu ba shine zai zamo rashin samun ilimin su ba, shiyasa aka ajiye gurbin karatu kaso 60 ga yara mata a makarantun Mega a jihar Borno.

Kwamishiniyar ta kara dacewa ana karfafawa manyan mata guiwa domin barin ‘ya ‘yan su mata suyi karatu.
Tace mata sun shiga damuwa matuka sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram wanda ya sanya su kama kananan sana’o’i da ayyukan noma domin biyan bukatun su.

Kwamishinayar ta kara dacewa an samu cigaba sosai a bangaren yawan matsalar cin zarafin mata sakamakon goyon baya da karfafawa da ake baiwa wadanda abin ya shafa daga ma’aikatar harkokin mata, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da kuma malaman addinai.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply