Gwamnatin jihar Taraba ta gargadi mutane musamman mazauna jihar dasu dena kone dazuka ba bisa ka’ida ba.

taraba-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Ahmed Umar Gosol, Taraba.
Gwamnatin jihar Taraba ta gargadi mutane musamman mazauna jihar dasu dena kone dazuka ba bisa ka’ida ba.

Hakan na cikin rahoton da sakataren yada labarai na gwamnan Iliya Bekyu Akweh ya fitar inda yace anyi gargadin ne don dakie hanyoyin gobara musamman a wan nan yanayin na bazara mai dauke da iska mai karfi.

Gwamnatin jiar ta bukaci kungiyar maharba ta jihar data dakatar da mambobinta musamman masu zuwa dajin dasu dena kone dajin don gudun yaduwar gobarar daji wadda na iya yaduwa sauran yankuna.

Wakilin Dandal Kura Radio International a Jalingo babban birnin jihar ta Taraba Ahmed Umar Gosol ya rawaito cewa gwamnatin jihar tace duk wanda aka kama ya karya dokar za’a hukunta shi yadda ya dace.

Haka nan yace rahoton ya bawa manoma harda masu noman rani shawarar su dinga lura da wutar don kare gonakinsu daga wutar daji.

Haka nan anyi kira ga iyaye dasu dinga kula da yaransu da abubuwan da sukeyi da han su wasa da wuta a wan nan yanayin da ake ciki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply