Gwamnatin Jihar Gombe Tace Ta Kammala Shirin Gina Kasuwanni 27 A Fadin Jihar Akan Kudi Kimanin Naira Biliyan 8.4

gombe 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Gombe tace ta kammala shirin gina kasuwanni 27 a fadin jihar akan kudi kimanin Naira biliyan 8.4.

Ya bayyana hakan a taron majalisar gwamnan jihar wanda gwamnan jihar ya jagoranta.

Ya bayyana cewa anyi taron hadin gwiwa da kwamishinan matasa da wasanni na jihar Julius Isaiah da takwaransa na cinikayya dad a yawon bude ido Nasiru Aliyu.

Isaiah ya bayyanawa manema labarai cewa majalisar fadar gwamnatin jihar tace zata kafa dokar t abaci a fanni sammar da ruwa, gyaran muhalli, tsafta kamar yadda gwamnatin tarayya ta bada umarni.

A nashi bangaren Aliyu yace majalisar gwamnan ta amince da kudi naira miliyan 370.3 na tsara aikin, shiryawa, yawan aikin dama kula da aikin a kasuwanni 27.

Haka nan ya bayyana cewa 10 cikin kasuwannin za’ayisu na zamani sai kuma 17 da za’a gyara.

Kwamishinan kasuwanci da yawon bude idon yace yayin yanke hukuncin dukkanin masu ruwa da tsakin na ciki.

Akan batun biyan diyya ya bayyana wa manema labarai cewa an gano cewa za’a biya kudade masu yawa kuma zasu cigaba da neman wasu guraren.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply