Gwamnatin Jihar Gombe Ta Kafa Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Billiri

gombe 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Gombe ta kafa dokar hana fita batare da bata lokaci ba zai fara aiki a karamar hukumar Billiri na jihar biyo bayan tashin hankali daya afku a yankin.

Sakataren gwamnan jihar farfesa Abubakar Njodi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da yan jaridu a jihar ranar jumma’a wanda yace saka dokar ya zama dole domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a wanda yace wasu bata gari sunyi amfani da damar zanga-zangar lumana sun tada hankulan jama’a

Ya kuma umarci hukumomin tsaron kasar da suyi aiki da dokar, sai dai wadanda aka bukaci ayyukan su kuma gwamnati jihar ta dage duk wani taron jama’a a karamar hukumar na Billiri.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya na NAN ta ruwaito cewa wasu mata a billirin sun toshe hanyar Gombe zuwa Yola da dalilin cewa gwamnatin jihar bata sanar da sabon sarkin Tangle ba kwanaki 3 bayan majalisar sarakunar ta mika zababben su ga gwamnatin jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply