Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum yace gwamnatin sa zata cigaba da zuba hannun jari a bangaren ilimi domin fitar da al’umma daga mummunar akidar yan ta’addan Boko Haram.
Gwamnan ya bayyana haka yayin kaddamar da majalisar gudanarwa na jami’ar jihar Borno karkashin shugabancin Dr Muhammadu Indimi.Gwamna Zulum ya gano cewa jami’ar wadda ta fara gudanar da ayyukan ta a shekarar 2019 ta zama abin amfani ga cigaban jihar.Ya bukaci shugaban da mambobin majalisar da su samar da hanyoyin da zai tabbatar da kyakkyawar gudanarwar harkokin makarantar.
Haka kuma gwamna Zulum ya bayyana manufar sa na kammala asibitin koyarwa na jami’ar jihar da kwalejin kiwon lafiya kafin ya kammala wa’adin mulkin sa.A cewar sa idan aka kammala ayyukan, asibitin zai taimaka wajen rage tafiye tafiyen harkar kiwon lafiya zuwa kasashen turai.
A nashi bangaren shugaban majaliar Dr. Muhammadu Indimi ya tabbatar da cewa zai habbaka jami’ar tare da kawo cigaba da dama.Kuma yayi alkawarin maida hankali kan ilimin mata, kuma a yanzu ya dauki nauyin dalibai mata dari 2 domin karantar bangaren kiwon lafiya a kasar Sudan.