Gwamnatin Jihar Borno Ta Ware Naira Miliyan 10 Domin Biyan Tsoffin Jami’an Tsaro Da Suka Rasa Rayukan su.

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta ware naira miliyan 10 ga jami’an sojojin da sukayi ritaya da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukan su.

Gwamna BG Zulum shi ya bada wannan umurni bayan an yi masa ado domin tunawa da ranar sojoji a gidan gwamnati anan Maiduguri.

Shugaban kungiyar tsoffin sojoji kanal William Mamza mai ritaya shi yayi wa gwamnan ado yayin da ya jagoranci jami’an tsaron wajen hotunan wadanda suka rasa rayukan su.

Yayin daya anshi bukatar kungiyar, gwamna Zulum ya bada umurni ga ma’aikatar noma da ta duba wani bangare wanda gwamnati zata iya taimakawa tsoffin sojojin domin sake samun filaye na nomad a aka basu.

Haka kuma sun bukaci motar noma daya amma gwamnan wanda yak ware a bangaren noman ban ruwa, yayi alkawarin cewa zai taimaka musu fiye da wanda suka bukata.
Daga karshe ya bukace su da suyi anfani da kayakin idan gwamnati ta basu taimakon.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply