Gwamnatin jihar Borno Ta Rufe Ofisoshin Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Guda 8 A Jihar

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamantin jihar Borno ta rufe ofisoshi 8 da kuma gidajen sauke baki na kungiyoyi masu zaman kansu a Maiduguri saboda basu bayyana takardun wuraren ba.

Da yake jawabi ga manema labarai babban sakataren hukuma mai lura da mallakin kasa da kiyaye dokokin ta ta jihar Borno Adam Bababe yace cikin kungiyoyi masu zaman kansu 183 da suke aiki a jihar nan, 21 ne kawai sukayi rajisata yadda ya dace.

A cewar sa hukumar ta rubuta wasiku da dama a watannin Yuni da Agusta na shekarar 2020 da kuma watan Janairun wannan shekara ga masu gidajen kungiyoyin amma basu mika shaidar mallakin ba.

Babban sakataren ya kara dacewa hukumar zata yi irin wannan aikin a bankuna da sauran wuraren kudade a fadin jihar nan.
Daga karshe yayi kira ga jama’a da abin ya shafa da su sabunta takardun.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply