Gwamnatin jihar Borno ta kwace aikin tituna na naira biliyan N6.7

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta kwace kwamngilar data bayar a farko ta naira biliyan 6 na gyaran tituna a cikin birnin jihar.

Kwamishinan ayyuka na jihar Alhaji Yerima Saleh ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda yace hakan ya biyo bayan bayan zaman majalisar zartaswa ta fadar gwamnatin wanda gwamnan Babagana Zulum ya jagoranta.

Saleh yace a ciki akwai titi mai nisan kilomita 20 da aka bayar a shekarar 2012 amma dan kwangilar kilomita 7 kawai yayi.
Haka nan yace sun wuce duk abubuwan da akayi yarjejeniya dasu akan aikin titin Bulumkutu magudanan ruwa da kuma titin kwalejin Ramat zuwa Wulari .

Inda yace a yanzu aikin titin daga Ramat din zuwa Wulari an bada shi ayi akan naira miliyan 230 million inda dan kwangilar zai dawo da naira miliyan 659.3.

Saleh ya gargadi yan kwangilar inda yace wan nan umarni ne daga gwamnati cewa baza su dauki rashin gudanar da ayyukan da aka bawa mutum ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply