Gwamnatin Jihar Borno Ta Karfafa Matasa 47 A Harkan Noma

farmers-at-work-agriculture
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta karfafa a kalla matasa 47 cikin shirin bangaren noma na N-Agriprenuears a jihar.

Kwamishinan noma da albarkatu, Engr Bukar Talba tare da hadin kan kungiyar kasar waje na asusun noma, dama na shirin sana’ar noma Agribusiness Support Programme ne suka kaddamar, tare da rabiyar kayayyakin aiki ga matasa masu sana’ar noma a jiha.

Gidan rediyo Dandal Kura International ta ruwaito cewa an kaddmar da bikin ne a harabar ofishin Bosap.

Engr. Talba ya bayyana cewa kayayyakin aikin da aka raba zai taimaka wajen samar da ayyuka tsakankanin matasan birni da na karkara kuma yabasu damar fara sana’o’I inda yace kashi 90 na al’umman jihar Borno suna noma.

kwamishinan yace gwamnatin jiha ta kirkiro da shirin noman shinkafa dama kamfani duk da nufin bunkasa amfanin gona a jihar.

Kuma yace cikin lokutan nan, sana’ar noma a jihar Borno ya samu cikas wanda ta’addancin Boko Haram ya haddasa hakan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply