Gwamnatin Jihar Borno Ta Kaddamar Da Wani Kwamiti Mai Karfin Gaske Domin Tantance Bayanai Malaman Makarantun Sakandire A Fadin Jihar.

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta kaddamar da wani kwamiti mai karfin gaske domin tantance bayanai malaman makarantun sakandare a duk fadin jihar.

Mataimakin Gwamnan, Alh.Umar Usman kadafur, wanda ya jagoranci bikin, ya ce tantance zai inganta harkan koyarwa a makarantar sakandare.

taron wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnati a nan birnin Maiduguri, Mataimakin Gwamnan ya bawa kwamiti umarnin tantance bayanan malamai da kuma duk wani abin da kwamitin zai ga ya dace da ka’idojin aikinsa.

Mataimakin Gwamnan, ya ce an zabi membobin kwamitin ne bisa la’akari da kwarewar da suke da ita, a sabo da haka, ya bukace su da su ba da jajarce wajen gudanar da aikin. ,inda kuma yace an basu watanni uku domin kammala aikin kamar yadda aka tsara.

Da yake jawabi a madadin mambobin babban kwamitin, shugaban kwamitin Farfesa Suleiman Bello, ya yaba wa gwamnatin jihar kan kokarinta na sake fasalin a bangaren ilimi tare da yin alkawarin gudanar da aikin kamar yadda aka umurta.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply