Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kaddamar Da Gangami Domin Rigakafin Dabbobi Miliyan 2.

map-of-bauchi-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da gangami domin rigakafin dabbobi miliyan 2.

Yayin da yake Magana a wajen kaddamar da kauyen Galambi a karamar hukumar Bauchi, Istifanus Irimiya daraktan bangaren dake kula da lafiyar dabbobi yace za’ayi hakan ne domin rage cututtuka a tsakanin dabbobin a jihar.

Yace cututtukan sun hada da pneumonia, helminthiasis, Contagious Vovine Pluro Pneumonia da Anti Rabies.

Yayi kira ga masu kiwon dabbobi da su bari a yiwa dabbobin su rigakafi.
Yace za’a gudanar da aikin a kananan hukumomi 20 dake fadin jihar kuma a gyauta.

Kuma rigakafin na da hadin guiwa da ma’aikatar noma na tarayya da hukumar lafiyar dabbobi na duniya.

Gwamnatin jihar Bauchi ta karbi rigakafin anti rabies dubu 6 daga gidauniyar yaki da cutar, domin yaki da cutar na rabies.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply