Gwamnatin jihar Bauchi Ta Gana Da Shuwagabannin, Da Daraktoci Na Cibiyar Kiwon Lafiya A Mataki Farko.

map-of-bauchi-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Bauchi ta gana da shuwagabannin, da daraktoci na cibiyar kiwon lafiya mataki na farko da kuma sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 20 na jihar kan tsarin biyan albashi.

Yayin da yake Magana wajen taron da akayi a babban dakin taro a gidan gwamanti, shugaban kwamiti kan tsarin biyan albashi Alh. Umaru Sanda Adamu ya yaba da hadin kan mahalarta taron.

Umaru Sanda Adamu kwamishinan kudi da cigaban tattalin arziki yace jihar tana kokarin tabbatar da an kawo karshen duk wani nau’I na zamba cikin tsarin biyan albashi da pansho.

Yace duk wanda aka sanya shi domin gyara a bangaren dole ne ya yi abinda ake bukata domin kiyaye abubuwan da basu dace ba.

Kuma yai kira a gare su da cewa a matsayin sun a shuwagabannin kananan hukumomi ya kamata su fitar da ma’aikatan bogi domin bada dama ga gwamnati wajen dauka wadanda suka dace aiki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply