
Gwamnatin jihar Adamawa ta fara gina kananan asibitoci masu filin daukan gadaje sittin a kanannnan hukumomin Lamurde, Gombi, Shelleng da kuma Girei bayan sake gyaran wasu dake mubi da kuma babban asibitin jihar dake Numan.
Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri shine ya bayyana hakkan a yayin da yake kaddamar da ayukkan gyara da akeyi a Ganye da kuma kuma babban asibitin jihar dake Numan.
Yace daya daga cikin kudurorin gwamnatinshi shine na samar da hanyoyin kiwon lafiya mai daurewa ta hanyar daukan kwarrarun ma’aikata.

Gwanana Fintiri ya kuma yaba da kokarin da hukomomi masu zaman kansu sukeyi a bangaren kiwon lafiya a cikin jihar.
