Gwamnatin Faransa Za Ta Fara Wani Shiri Domin Inganta Tattalin Arzikinta A Afirka.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin Faransa za ta fara wani shiri na Euro biliyan biyar don inganta dangantakar tattalin arzikinta a Afirka.

Ministan Harkokin Wajen Faransa Mista Franck Reister ya bayyana haka bayan wani taro tare da Kungiyar Gwamnonin Najeriya a Abuja.

Amfanin ganawar na kwanaki biyu da Ministan ya yi shine don karfafa alakar da ke tsakanin Faransa da Afirka da Najeriya a matsayinta na babbar kawarta a nahiyar.

Ziyarar ta biyo bayan abubuwan da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanya a gaba yayin ziyarar da ya kawo Najeriya a watan Yulin shekarar 2018 da kuma aniyarsa ta karfafa alakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa.

Ministan Harkokin Wajen na Faransa ya ce Najeriya ita ce abokiyar kasuwancinsu ta farko a yankin Saharar Afirka tare da cinikayyar bangarorin biyu na dala biliyan 4.5 a shekarar 2019 wanda ya ragu zuwa dala biliyan 2.3 saboda matsalar 19.

Mista Riester ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai kasance a cikin kamfanoni masu zaman kansu da na jama’a ta hanyar hukumomin Cigaban Faransa.

Ministan na Faransa ya bayyana kudurin Faransa na kara jarinsu a Najeriya ta hanyar samar da rancen dala biliyan biyu don tallafawa bangarori masu zaman kansu da na tattalin arzikin Najeriya.

Taron wanda shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya jagoranta ya yabawa Gwamn

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply